Thursday, 28 March 2024

Select your language

Tracts

Ceto Tawurin Mafarki -  Biyu

Ceto Tawurin Mafarki -  Biyu

Labarin Khalil

Khalil Ya fara koyarwa  karatu al’quaran tun yana Karami. Yayi girima da son maganganun Allah.

Ya fara karatun litatafi Islamiya da ma’anar quran. Da Khalil Yana kebe musulim da mara musuluchi yanda aka koya a Q’uran , Ya mai da mahaifin shi  marasa amana. Ka’nan  abu kamar mache   bata rufe kainta ba sai ya  maida ita  marasa amana yan da shi ya gane qu’ran ke nan. In ya gani namiji musulimi mara gemu, a ganin Khalil,  shi ba musulimi ba ne. Duka masu bi Kriista ya mai da su baban matsiyachin shi. Ya hada hanu da masu kashe Kristochi da kunerwa ikilisiya su. Kungiya Islamiya dake jamiya Masar sun zabe shi  shugaban jamiya musulimi da zasu yi fada dasu  Krista. Wanan kungiya musulimi da Khalil yake shi ne shugaban su , suna sata mutane  masu rubutun wadan da sun rubuta abinda baya so.

Daga baya, Sojoji Masar sun kama Khalil: Ya yi shekara biyu a kurkuku an bashi wiya sosai.  Da aka seke shi, ya bar Masar tare da  sauran ma su bin shi.

Ya karanta a Litafi mai Labari cewa an kama wasu masu bi Krista a Cairo don suna wa’azi. Khalil da masu binshi da suka ji haka, sun kasanche cewa ya kamata su ma su yi wani abu a suna Islam. Damin basu da yawa,  sun yarda  fada da zasu yi dasu Krista na Ilimi ne. Khalil ya fara rubutawa Litatafai ya tabarta musu cewa Mohammed ne  gaskiyan annabawa na Allah; da kuma Litafi Mai Tsarki na Krista da na su Yahudawa mugun litafi ne.

Sarki garin, shugaban makartan  Islamiyan   ya zabi Khalil cewa shi ne zai nemi yar da zai rubuta wanan Litafi. Khalil ya ki  wanan aiki da karfi da farko, daga baya ya doka aikin da bakin ciki. Da ya gama karatan litafi Mai Tsarki  ya Kwantata shi da litatafe Islamiya  da yawa,  Khalil yayi  mamaki  da samu cewa litafi mai Tsarki  bata karance gaskiya ba, kuma ba Litafi mai bataccen hankali ba. A binda ya bashi mamaki kuma shi ne, koyarwa gafartawa masu laifofi, kaunan mara iyaka yanda Yesu ya nuna a zaman shi a duniyada maganganu shi a  litafi Mai Tsarki. Abinda ya fi tunanin shi ne yanda Yesu ya bayana ma mabiyansa cewa mutane zasu tsanantar dasu. Bayan shekara dubu biyu maganan shi ya zama gaskiye kamar yarda ya fada. Litafi Mai Tsarki da ya karanta ya bude mi shi Iddo, hali su Krista da suka mugunta musu a Masar da ba su rama ba. Ya kuma gan dalilida yafewa da mantuwa su Krista,  muguntan halinsu musulimi ba dai wiya ba. Yar  da yana kiyaye karantu Litafi Mai Tsarki, ya na kuana labarin da koyarwa da ke cikin shi.

Ko da yake, ya ci gaba da aikin shi da  bai gama. Yana kokari ya amince Yesu ba Allah ba, da  ba a gicciyeshi ba. Khalil yana himmanta  da Qu’ran domin wanan dalili. Ya tara duka hankali yar’da Qu’ran ya surare. Sun dubi hankali Yesu kamar yar da ake rubuta a Qu’aran. Sun samu cewa a Qu’ran Ubangiji shi kaide ne mai halittar, mai wakarsuwa mai Badawar. Shi kaide  ne mai tar da matattu da mai mu’ujizai. Shi ne kawai mahukunchi mai adalci.    Khalil ya gamu da abun mamaki, da koma cikin Quaran ya samu  cewa, kebaben  Hali na Ubangiji shi ne Yesu . Wanan ya nuna  ma Khalil cewa Ubangiji da Yesu Duk daya ne.

A rana daya, Sarki ya zo ya gaishe shi a gidan shi. Ya karanta duka rubutu da Khalil ya yi (Adalcin Yesu, da Qua’ran ba bubutun Allah ba) bai  yarda da abin da ya karanta ba. Ya gayawa Khalil shi zai kashe shi indan  ya nuna wa musulumi duka rubutun shi daya karanta a wajen shi. Daga wanan lokoci, ya mar da Khalil Ar’ne.

Ko da yake,  Khalil  bai iya ya bar sabobin  koyarwa da ya samu cewa Kristanci shene  gaskiyan hanya.  Ya yi kokari ya kara himman wannan hanya saiya hada kain sa da ikilisiya. Don muguntan hali shi na da, mutane basu karbe shi da hannu biyu ba. Ama Ruhu ya yi mishi Magana cewa kar ya kali mutane ya cigaba da hanya bi. A kwai wata rana da Khalil yaje  yayi waya Sai an sata karamin jakan shi da yana daura a jiki. Duka sabon rubutu da yayi, Litafi Mai Tsarki na shi da  hoton shi a cikin jaka da a ka sata.

Tsoro ya kama shi don abubuwa daya rubuta a cikin jakan. Idan musulmi sun hangi abinda ya rubuta za  su kashe shi. Ya gudu ya je gida tunaninshi  ya razanar dashi.  Yayi al’wala ya fito da taburma ya yi sallah. Ye sunkuya, ya, zama mashi wahala, bakin shi bai budu  ba,ko kalma daya na Qu’ran bai iya ya fada ba. Ya ce “Ubangiji  ka sani ina kaunan ka,na san  ka na so in bi hanya mai gaskiya. Ubangiji ba  zan iya In tsanata ka da kai ba. Duka abubuwa da na yi nayi domin In kwatata Kaine. Ina roke ka ka cire ni  daga wannan duhu.”

A dare kwana nan, Khalil ya yi barchi kamar yanda ba yayi a sauran shekaru  da suka wuce.  A mafarki, ya gani wanni  mutun da yana magana da shi cewa shi  ne mutum da Khalil yana nema. Khalil bai san wanna  mutun ba. Mai Magana da shi ya gaya mishi cewa, idan yana so ya san mai Magana dashi, ya  duba  Litafi Mai Tsarki, shi kuma ya amsa cewa ai litafi da sauran takardu na  sun bace, mutumin yace mishi “litafin bata bace . Ka tashi ka duba  cikin waje ajiyar kayan ka, zaka samu litafi a wurin. Sauran tarkardun ka zasu dawo  a karshe wannan  sati.”

Khalil ya tashi daga barci ya bude waje agiyan sa. Lalai ga Litafi mai Tsarki Shi a kwance. Sannin cewa shi ya gan Yesu, ya tashi a guje  zuwa dakin uwarsa. Ya tashe ta daga barci yana rokon gafara daga hanun ta, domin muguntan  da batance hali shi da ita, da su Iyali. Tambaya gafara bai kare da iyali kaide ba. Da gari ya waye  ya shiga cikin gari yana gaida mutane, abokane da bako,  Yaje wuri Krista masu tala. Ya ce su gafarce shi don kayansu da, ya sata, ko mugun hali shi a wajen su.

A watan da suka wuce, Khali ya kara girma a sabon hanya, Nan  da nan ya fara samu karfin zuchiya, Sauran Ikilisiya sun bude mishi Kofar. Aka yi mi shi baftisma ya cigaba da hanya bi. Ko dayeke, baiyi tattalin rainshi ba. Tunanin  shi nawa ne zai iya ya biya  ma Ubangiji da bada duka abubuwa ma shi.

Popular Items //fa-pencil

Newsletter

Subscribe to our newsletter to get the latest updates from House of Karis

House of Karis Logo Footer

The House of Karis is a Christian publishing house focused on providing pure and truthful information that shall enable Christians live in righteousness and in the fear of God.

Email: bosun@houseofkaris.net

Search